Zaghawa

Bikin auren gargajiya na yan kabilar ta Beri_"Zaghawa"
hoton bikin auren zaghawa

Mutanen Zaghawa, ana kuma kiran su Beri ko Zakhawa, ƙabilun Musulmin Sahelian ne waɗanda ke zaune a Kudancin Libya, gabashin Chadi, da yammacin Sudan, ciki har da Darfur.

Zaghawa suna magana da yaren Zaghawa, wanda shine yankin Saharar gabas. [1] Makiyaya ne, Kuma irin garken tumakin da suke Kiwata larabawa ke kira Zaghawa. Su makiyaya ne kuma suna samun yawancin abincinsu ta hanyar kiwon shanu, raƙuma da tumaki da kuma girbin hatsin daji. An Kiyata cewa akwai tsakanin 4,000,000 zuwa 4,512,000 Zaghawa. [2]

  1. Zaghawa, Ethnologue
  2. Zaghawa survey, SIL Chad. 2004.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search